Kutse da Kariyarsa

Kutse Da Kariyarsa

Duba da yadda ba mu da littafin da ke bayani a kan kutse (hacking) da kariyarsa (protection) a harshen Hausa hakan ya sa na dan tsara wannan talifi domin yin gutsuren da zai wayar da kan al’ummarmu game da kutse, masu kutse, na’uikan kutse, kayan kutse da kuma yadda za su kare kansu.

A cikin wannan littafin mai suna ‘Kutse da Kariyarsa’ na fara da yin bayani a kan menene kutse kuma waye makutsi, sa’annan na gangaro zuwa nau’ikan makutsa da kuma nau’ikan hare-harensu da yadda mutum zai kare kansa daga irin hare-haren kutse.

Na kuma dan kara zurfafawa ta hanyar bada misalai na irin kayayyakin da ake yin kutsen da su. Kazalika na yi iya yi na wurin kiyaye ka’idojojin rubutun Hausa a cikin talifin.

Za ku iya saukar da littafin da littafin ta Okadabooks ko shafin nan nawa:

getButton} $icon={book} $text={READ ON OKADABOOKS}

getButton} $icon={download} $text={DOWNLOAD PDF}

Amma fa duk rintsi wannan littafin kyauta ne, ba na siyarwa ba ne, don haka za ku iya rarrabashi kyauta ga sauran al’umma dan su ma su karu. Don haka dan Allah kada wani ya siyar da shi.

Abba Abdullahi Garba

1 ga watan Muharram, 

2 ga watan Aprilu, 2022.

Abba Abdullahi Garba

Abba Abdullahi Garba, AKA Zugson, is a Nigerian upcoming artist and songwriter, tech bro, part-time blogger, and writer.

Previous Post Next Post