Jiki Magayi: Hankada Mai Kan Tururuwar Da Baba da Emeifele Suka Mana a Kan Canjin Kudi

Duk sonka da son sai ka gyara al’umma muddin ka rasa mataimaka na gari, lallai za ka jima kana tufka ta gaba ta baya na warwarewa.

Masu iya magana sun yi gaskiya da su ka ce,”Mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi sai ya gani, kuma kamar yadda gani ya kori ji, to shi ma jiki magayi ne.”

Kwarai da gaske wadanda Allah Madaukakin Sarki ya sa za su ga wannan badin kam gashi za su ganta, wadanda kuwa rai ya yi halinsa kafin su kai ga ganinta na yi imanin sun jima da iske su mujaddadi.

Lokaci na farko da na ji labarin za a yi sauyin kudi kuma na kalli cikakkiyar tattaunawar da Tambarin Hausa TV ta yi da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da kuma matsayarsa hadi da furucinsa game da canjin kudin nan, abin ya matukar ba da citta har ta kai cewa na ji dadi da wannan gagarumin canji da gwamnati ke son yi domin canji ne wanda ke tafe da makarkashiyar siyasa, dakile almundahana hadi da amsar juyin-juya-halin fasaha.

Sai dai ba ta nan gizon ke saka ba!

Rayuwa ta ci gaba da tafiya kamar yadda ta saba, wannan ya wuce.

Bayan wasu kwanaki fadar shugaban kasa ta kaddamar da sabuwar Naira (₦) wacce asalin bugawar Najeriya ce sabanin sauraran kudaden kasar da suka

Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah! Mu kwana mu tashi ranaku da awanni na shudewa har ranar da babban bankin tarayya ya fara sakin sabuwar Naira wa bankuna ta zo.

Hankalin mutanen birane, karkara da kauyuka ya matukar tashi kwarai da gaske sakamakon labarai iri-iri da suka yi ta yawo game da wannan canjin kudi, kai har ta kai ta kawo duk wanda ya san ya boye tsoffin Nairori sai da ya fito da su ya kaisu banki aka dura masa lambobi a akawun.

‘Yan kasuwa su ma ba a barsu a baya ba wurin kai kudi banki, kai har ma da ya-ku-bayi irin mu, kowa ya san yadda zai yi da kudinsa. In mutum bai kai banki ba ko ya ba mai P.O.S ba to ya je kasuwa ya yi sayayya a kan farashi mai tsada.

Abubuwa dai suka hadu suka rincabe, suka yi wa mutane yawa, kebur ko-ta-ko-ina zabgarsu yake. Layi a banki, wulakancin masu gidan mai da tsadar fetur, wulakanci da tsawwalawar masu P.O.S, tsawwalawar masu sayar da kayan masarufi, wulakancin ‘yan kasuwa, iskancin masu sana’a da dai sauransu. Talaka har ma da masu rufin asiri suka zama ababen tausayi. Zulumi da damuwa suka dabaibaye al’umma. Kai koke-koken rashin sabon kudi a banki ya yawaita. Abubuwa dai su ka hadu su ka cakude, ba ko kyan gani bare dadin labari.

Al’umma su ka ci gaba da zarya a banki, suna kai tsohon kudi ana dura musu lambobi a akawun, kuma ATM ba ya yin amon sabon kudi. To, a wannan lokaci ne mutane suka fara zargin manajojin banki kan anya ba masu hannu da shuni su ke musanyawa tsoffin kudadensu da sabbin da CBN ta basu suna karbar kaso 5 zuwa goma daga ciki ba?

Alamomin tambaya, zargi da kuma rashin yarda su ka kara yawa a kan manajojin banki, har ta kai ta kawo mutane su ka yi imanin cewa; ana kawo kudi banki, kawai talaka ne ba a son a baiwa sai masu abin sun wadata tukunna.

A haka dai, ‘ya-kwance-uwa-a-dimauce kwanakin da CBN ta yanka su ka ci gaba da shudewa. Kullum talaka kuncinsa karuwa ya ke, matsin da ya ke shiga karuwa ya ke. Harkoki kara tsayawa su ke har ta kai ta kawo kafin ranar 31 ga watan 2 mutane ransu ya fi na san huda baci. Wa’iyazubillah.

Jita-jita, kunji-kunji, kace-nace, karairayi da labaran bogi a soshiyal mediya su ka dada rura wutar bala’in da mutane suka shiga. Ya zamana cewa an fada dumu-dumu cikin kaka-na-ka-yi.

Shi ma gwamnan CBN da Shugaba Buhari hadi da gidajen jaridun yanar gizo da zahiri har ma da gidajen rediyoyi su ka cigaba da tunzura mutane kan cewa an fa yanke ranar daina karbar tsohon kudi saboda haka babu-gudu-babu-ja-da-baya.

Nan mutane sun gama sakankancewa kan za a yi ta ta kare, wato ranar 1 ga watan biyu tsofin kudi za su zama marasa amfani, wasu kuma sun zage da koke-koke da kiraye-kirayen a daga ranar dena karbar tsohon kudi. Kwatsam sai ji aka yi labari ya fito daga fadar shugaban kasa kan cewa Emifeile ya samu Buhari sun tattauna sun yanke shawarar kara wa’adin kwana 10 na daina karbar kudin.

WAUTAR WASU TA FITO FILI

A wautar wasu mutanen, wai su ba su ji dadin dagawar nan ba, sun fi son a yi ta ta kare alhalin ba su san cewa su ne za su ci kaniyarsu ba.

Kuma rashin son bincike-bincike da bibiyar masu bincike ta fanni daban-daban ta kafafen sada zumunta shi yasa mafi yawan mutane suka rude, rudewa mai girman gaske. Domin in ba zan manta ba, wani dalibin shari’a, Shehu Rahinat Na’Allah tun kafin wannan lokacin ya fadi .

Mutane da dama sun yi tunanin wannan dokar da ya zayyano ta canjin kudi a Najeriya ba za ta yi aiki ba sakamakon wasu dalilai da na nazarta daga ra’ayoyin mutane kamar haka;

1.    Buhari ya taba canjin kudi yayin tsohuwar kifaffiyar gwamnatinsa.

2.    Bai kuma daga kafa ba, cikin sati biyu ya canza kudin.

3.    Mutane da dama sun karye, wasu sun tsiyace dalilin hakan.

4.    Kuma tattalin arziki ya matukar jijjiga kwarai da gaske.

To, wadannan dalilai su suka sa mutane suka rude game da canjin kudin nan, har ta kai ta kawo sun manta da cewa; Buhari fa yanzu ba mulkin soja ya ke mana ba, a’a, mulkin dimokuradiyya ya ke mana, ita kuwa dimokuradiyya ba a cika mata karantsaye ba, komai bisa tsari da amincewar majalissa da al’umma ake yinsa.

Haka zalika, Shugaban mulkin farar hula bashi da ikon yi wa wasu dokokin kasa hawan-tsaye musamman wadanda suka shafi baki dayan ‘yan kasa har da masu uwa a gindin murhu.

HARKA TA TSAYA CIK

Masu harka kam na can suna yin kayarsu, masu ‘yar harka ma haka. To amma fa canjin kudin nan ya matukar tsayar da gudanar al’amuran yau da kullum kwarai da gaske.

Kuma duk wanda ya budi baki yace ma karya ne, ka ce iyatai, in ya musa maka ka ce ni na ce fadi hakan. In kuma kuli-kulinka zai yi to ya yi.

MUN YI WA DOKA GURGUWAR FAHIMTA

Mafi akasarin mutane sun yi wa doka gurguwar fahimta. Wasu gani suke in dai ka kai wani mataki to babu yadda za a yi da kai, alhalin a zahirin gaskiya sai dai in kyaleka aka yi.

Yadda muka dauka shi ne; doka ba za ta taba yin aiki a kan wasu mutane ba, kuma ba haka ba ne. Domin da ba doka ce ta nada Emeifele ba lallai da bai bayyana gaban majalissar dattijai ba da ta kirashi, kuma da bai fayyace gaskiyar lamari ba (wato abinda matashin dalibin nan ya fadi).

AN ZALUNCI TALAKAWA FA!

A nan kam babu wani boye-boye ko kwalo-kwalo, zallar cuta dai an yi wa malam talaka ita. Kuma dama ko me za ka yi da jaki sai ya ci kara. Mu ‘yan Najeriya mafi yawancinmu cike muke da son kanmu.

Kaga bala’in da zai sa ka rike lambobi a kati amma babu kudin siyan kayan masarufin kaiwa iyali ai ba karami bane.

Saboda haka duk wanda ya bayar da gudunmawa wajen zaluntar malam Shehu to fa ya sani bai ci lalai ba. Domin ka yi da kyau ma ta karshe ma balle ka zama zalimu?

Mu dai mun bar komai ga Allah ya isar mana.

IN BERA DA SATA…

Tabbas ba a shege daya sai dai shegu, kuma in bera da sata to daddawa da wari. Mu kanmu mafi yawancin talakawa ba mu da kirki kwarai gaske. So muke yau ace ranar mu ce domin mu sha jinin ‘yan‘uwanmu mu yi tatil.

Da Dan Alu ya samu dama aka ce yau fa kowa ta shi yake, to sai shima ya yi ta surfa tsiyarsa yadda yake so. Ba ruwansa da ya kamata, a’a, shi kawai ta ya ya zai tattaka ya dare sama shi ne burinsa.

Saboda haka in shugaba da zalunci, to, shi ma malam talaka da son zuciya tattare da shi. Kowa na bidar sauki wurin siya, in ko shi zai siyar babu ruwansa da saukakawa, a’a, ya fi son in da hali ma kayan ya ninka kudinsa.

To, ta ya ya za mu cigaba muna rike da irin wannan muguwar dabi’a da akida? Ta ya ya shugabanni za su ji tausayinmu alhalin mu kanmu ba mu da tausayin ko digo?

Akwai gyara fa!

AN BURMA MU A KAN CANJIN KUDIN NAN.

Kwarai da gaske an matukar burma mu, mun fada sai dai fatan Allah ya kawo mana sauki.

Tsoffin kudadenmu har kwanan shekara mai zuwa suna nan a matsayin kudade, kawai dai in sun shiga banki ne ba za su fito ba.

Ni dai shawara garemu ita ce, “Mutane su kokarta fara karyar transfer na kudi muddin transaction ya wuce 10k domin ga dukkan alamu manyan kudade ba za su kara yin mahaukaciyar wajajata kamar yadda suka yi a baya ba.”

“Wadanda basu a asusun bankuna, su kokarta zuwa su bude, masu sana’o’i da ‘yan kasuwa su kokarta karbo P.O.S daga bankunansu domin cigaba da gudanar da kasuwancinsu cikin salama.”

“Mu kuma yi takatsatsan da dukkanin wasu bayananmu da suka danganci banki, kada wanda ya kiramu muka bashi bayananmu masu muhimmanci kamar su BVN, lambobin kati, tura lambobin da aka aiko da message da sauransu.”

A karshe ina matukar jajanta mana da fatan Allah yasa hakan ce ta fi alkhairi.

Abba Abdullahi Garba

Abba Abdullahi Garba, also known as Zugson, is a Nigerian upcoming artist and songwriter, tech bro, part-time blogger, and writer. He is the writer of his own songs as well as his own story.

Post a Comment

Previous Post Next Post