Hmm! Kai Dai Ka Ga Mutum

Kamar yadda yatsunmu ba su kasance daya ba, haka ma al’adarmu, tarbiyyarmu, kula da addininmu, kamalarmu, sanin ya kamatanmu, hangen nesanmu da sauran al’amura na rayuwa ba daya suke ba.

Sai dai na fahimci wasu mutane sun yi wa wani bangaren na rayuwa baragurbin fahimta.

Gani suke in dai ba su ba to fa ba wani wayayyen taliki, wanda ya san rayuwa ya san me ya ke sama da su, ba su tsayawa yin binciken ko waye wannan talikin, ko menene matsayinsa? A’a gaba-gadi suke yankewa talikai hukunci,

Ban yi mamaki ba kwarai da gaske, domin na tabbata ni ba wani ilimi gare ni ba, kuma ba wani wayayye ne ba, kamar yadda suka sha fada min, kuma na yi imanin mai yi baya fada sai dai aga aiki da cikawa.

Ba fa wani abu bane wayewa face, tsantsar disashewar kunya tsakanin talikai, duk wanda kunya ta disashe daga fuskarsa to fa wannan ya gama cika wayayye. In kuma wayewa ce ta fannin addini to lallai mai ilimi, dalibin ilimi, da mai son zuwa daukar ilimi su wadannan bayi sune wayayyu.

Abin kam akwai sa takaici kwarai da gaske, to amma ya na iya? Bisa dole na bagaras domin mu yi zaman mutunci da mutunta juna tsakani na da su.

Ni ban kasance kowa ba, face wani yaro mai karancin shekaru, dan wani karamin kauye da ke Kasar Najeriya.

Dan’uwa kada ka kasance cikin jerin mutane masu yanke wa mutane hukunci gaba gadi ba tare da ka yi babban bincike akansu ba.

Shawara ce kyauta na baka.

Abba Abdullahi Garba

Abba Abdullahi Garba, also known as Zugson, is a Nigerian upcoming artist and songwriter, tech bro, part-time blogger, and writer. He is the writer of his own songs as well as his own story.

Post a Comment

Previous Post Next Post