Ainihin Kudin Aikin Hajjin Bana (Shekarar 2024)

Mahajjata Mata
Mahajjata Mata


Duba da irin sauye-sauyen da ake samu, ga kuma rayuwa kullum tsadarta tsananta take yi shi yasa hukumar jin dadin alhazai ta gaza tsayar da tsayayyen farashin kudin aikin hajji.

A tsakanin shekaru 13 an samu karin kudin zuwa aikin hajji har ma da na Umara ba kadan ba.

Adadin kam ya ninka ya kai sau wajen bakwai.

Misali: a shekarar 2013, kudin aikin hajji ₦600,000 ne a karamar kujera, babbar kuma ₦700,000.

Yayin da a 2015 kuma ya kai ₦766,000, matsakaiciyar ₦800,00, yayin da babbar kujera ta kai ₦900,000.

Zuwa shekarar 2022 kuma kudin aikin hajji ya kai ₦2,500,000.

To, in muka yi duba na tsanaki, za mu ga cewa, ashe yanzu zamani ba karamin sauyawa ya yi ba.

In baka da anini, to ba ka isa zuwa hajji ba, amma in har ka tara, kuma Allah ya hore maka, to yana da kyau mutum ya kukkuta ya je din domin ya sauke farali.

Kudin Aikin Hajjin Bana (2024)

Kudin aikin hajjin bana, na shekarar 2024 a babbar kujera ya kai akalla miliyan hudu da doriya kamar yadda hukumar jin dadin alhazai ta kasa ta bayyana.

Yayin da a shekarar 2023, kudin bai wuce miliyan biyu da rabi ba. 

Kammalawa

Domin sanin ainihin kudin aikin hajjin bana, ka kuma zabi kujerar da kake son biya, zai fi kyau ka ziyarci ofishin jin dadin alhazai na jiharku domin samun isashshen bayani.

Tambayoyi Masu Alaka

kudin aikin hajji 2023, kudin aikin umrah 2022, kudin aikin hajjin bana, kudin aikin hajji 2022, kudin aikin hajji, kudin aikin hajjin 2023, kudin aikin zabe, nawane kudin aikin hajjin bana. nawane kudin aikin hajjin bana 2023, nawane kudin aikin hajjin 2023, kudin aikin hajji 2023, kudin aikin hajji 2023 nigeria,kudin aikin umrah 2022, kudin aikin hajjin bana


Previous Post Next Post