Menene Ma'anar Noma (Tushen Arziki)

Noma
Noma


Hakikanin gaskiya in dai ba zamani ne ya ci amanar al'ummar Hausawa ba, ban ga ta yadda za su aje sana'ar noma ba dungurungun dinta.

Domin su dama can Hausawa da noma aka san su, Fulani kuwa da kiwo. 

Sakamakon cakuduwar Hausawa da Fulani a inuwa daya, hakan ya kara habbaka noma da kiwo da kuma auratayya a tsakaninsu duk da har zuwa yau akwai Hausawa da Fulanin da ke fada akan Burtali da cin iyaka.

"Noma wata hanya ce wacce ake bi don samar da abinci da abin sha da kuma kudin shiga."

Kuma noma na da matukar tasiri wurin tabbatar da dogaro da kai hadi da habbaka tattalin arzikin duk al'ummar da ta raja'a akan sa.

Wannan dalili ya sa zan dauko baitin wata waka (na manta sunan mawakin) akan noma.

"Noma tushen arziki, ayi noma yaki cigaba."

Haka kuma zan tuno mana da wani kirari da ake yi wa noma

"Na duke tsohon ciniki, kowa ya zo nan duniya kai ya taras."

A wajen Hausawa musamman mazauna karkara har ma da na Birane, noma ya zama wajibi (dole).

Kuma da wuya ka samu cikakken bahaushen da bai san noma ba, kuma bai iya shi ba.

Previous Post Next Post