Menene Ma'anar Rubutacciyar Waka a Harshen Hausa

Ma'anar Waka


Kusan duk wani wanda ke ji da kuma juya harshen Hausa ya san wasu daga cikin wakokin Hausa, in bai san na gargajiya ba irin su wakokin (Shata, Sani Sabulu, Ali Makaho, Shago) ba, to ya san na zamani irin su Mahmoud Nagudu, Nazifi Asnanic, Dauda Kahutu Rarara, Nura M. Inuwa da sauransu.

To, amma menene ma'anar waka rubutacciya?

Yanzu haka za ku ji ma'anar da masana adabin Hausa da dama suka bayar a kan waka rubutacciya. Za mu fara da ta'arifin Malam Bello Sa'id.

"Rubutacciyar waka ita ce wadda aka tsara, aka rubuta ta a takarda don a karanta." (Bello Sa'id:1981)

Shi ma Farfesa Sa'idu Gusau ya bada mana'ar wakar kamar haka a shekarar 2001

"Waka ta bambanta da tadi na yau da kullum. Abu ce da ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna kwarewar harshe. Harshen waka cikakke ne, duk da yakan kauce wa wasu ka'idojin nahawu." (Gusau:2001)

Shi ma Malam Mukhtar ya bada ma'anar waka kamar haka a shekarar 2006 inda ya ce:

"Rubutacciyar waka, wata hanya ce ta gabatar da wani sako cikin kayyadaddun kalmomi da aka zaba, wadanda ake rerawa a kan kari da kafiya a cikin baitoci." (Mukhtar:2006)

Shi ko Dangambo a shekarar 2007 ya bada ma'anar waka kama haka:

"Waka wani salo ne da ake gina shi kan tsararriyar ka'ida ta dango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (kafiya), da sauran ka'idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaben su da amfani da su, cikin sigogin da ba lallai ne haka suke a maganar baka ba." (Dangambo:2007)

Previous Post Next Post