![]() |
Minene Amfanin Soyayya |
Yau, abin da za mu tattauna akai shi ne kalmar “So”. Menene ma’anar wannan kalma a tsantsar tsagwaron tsararriyar rubutacciyar Hausa?
Kusan kowa dai ya san kalmar, yana amfani dai ita, to, amma ba lallai ya san ma’anarta ba gamsashshiya.
“Shi so wani irin shauki ne wanda ake jinsa a cikin zuciya game da mutum, kudi, dukiya da sauran abubuwa.”
Sai dai a iya dogon nazarin da binciken kwakwaf din da na yi, na fahimci shi so ya kasu ne gida biyu.
Akwai;
- Son Sha’awa
- Son Kauna
Menene Son Sha’awa
“Shi son sha’awa shi ne son da muke yi wa mutum ko wani abu na ‘dan lokaci saboda kyawu ko wani kyale-kyale da ke tattare da shi.”
Amma mazaunin son shi wannan abun da muka bashi a cikin zuciyarmu na ‘dan lokaci ne, daga lokacin da ya sauya siffa, kyawunsa ya disashe ko wani abu makamancin haka ya faru da shi sai mu ji mun daina son shi wannan abu.
Misali: Daga cikin dalilan da yasa aure ya cika saurin mutuwa a wannan zamanin akwai son sha’awa da maza ke yi wa matan da suke aura din, da mutum ya kwanta da ita daya, biyu, uku sai ya ji ta fita a ransa.
Menene Son Kauna
“Son kauna shi ne asalin gurguzun gangariyan so wanda ake yinsa har cikin kashin zuci, wani irin so ne wanda ake yinsa ba tare da duban wani kyale-kyale ko kyawu ba, wato da zuciya daya ake yinsa.”
Son kauna shi ne samfurin son da muke yi wa Allahn da ya hallicemu, da Annabinmu, da Addininmu, iyayenmu, iyalanmu da ‘ya‘yanmu, da dukiyoyinmu.
Yana daga cikin nau’in so mafi wahalar samu, amma duk ranar da mace ta yi nasarar samun wanda ke yi ma son kauna, to, lallai ta dace.
Allah shi kyauta.