Menene Maganin Sanyi (Sanyin Mara, Sanyin Kashi, da Sanyin Mura)

Maganin Sanyi


Amsa tambayar menene maganin sanyi ba karamin abu bace, kuma mai amfani.

A nan, sanyin da nake yi magana kowa ya san shi, ina nufin sanyin kashi, sanyin mara ko kuma sanyin da ke kama mutane suna yin mura.

“Shi maganin sanyi wani irin nau’in magani ne wanda ake sha domin neman waraka daga ciwon sanyin mara, sanyin kashi ko kuma sanyi wanda ke haifar da mura.”

Sakamakon mun kawo muku nau’ikan sanyi, hakan ba shi ke nufin ba za mu tsaya domin yu muku bayani akansu ba.

Sanyin Mara 

“Shi sanyin mara nau’in sanyi ne wanda ake kiransa da sanyin mata, mafi akasarin lokuta ana samunsa ne ta hanyar jima’I ko dalilin lalataccen maniyyi da ke daskarewa a marar namiji.”

Shi ne sanyin da ke haifar da kurajen gaba, kankancewar gaba, kaikayin gaba da sauran cututtuka.

In da ka fahimci ko kin fahimci kina dauke da ciwon sanyi, to kawai ki je wurin likita domin ya baki magani ko kuma ki gwada maganin gargajiya.

Amma fa a kula, ba kowanne maganin sanyi ake sha ba musamman na gargajiya saboda wani maganin zai matukar bata wa mutum rai yada bai yi zato ba.

Sanyin Kashi

“Shi sanyin kashi shi ne wanda in ya kama ka za ka ji gwuiwarka ta kafa tana rikewa.”

Da zarar ka ji gwuiwar kafarka na rikewa, kawai ka tafi ka nemi magani, kuma in da son samu ne, ka je ga likita domin ya duba ka ya baka maganin da zai dace da cutar da ke damunta.

A shawarce: in ka fahimci ka kamu da sanyin kashi, ka wuce kai tsaye asibiti ka ga likita. Domin magungunan gargajiya mafi akasarinsu cuta 100 ake lissafto wa kuma ace ai magani daya tilo duk yana maganinsu. 

Sanyin Da Ke Haifar da Mura

“Nau’in sanyi ne wanda ke sanya wa mutum ya kamu da mura, toshewar hanci, tari, kaki da sauransu.”

Shi kansa in dai ka fahimci ka kamu da shi, to, a shawarce ka je ka ga likita.

Kada ka bari kanka ya kulle ka tafi wurin maganin gargajiya ka rinka yin shan maganin da ba zai warkar da cutar da ke addabarka ba.

Kuskuren Mutanenmu

Na daga cikin manyan kura-kuran mutanenmu, su ne; rashin son zuwa ganin likita da zarar mutum ya fara jin sauyin yanayi a jikinsa.

Sai ya yi ra’as a gida, ya ki zuwa, ya yi ta shan sassake-sassake ba tare da ya san ainihin amfaninsu ba, sai yaji ba haza, sannan sai a kwaso shi rabe-rabe a tafi asabiti.

Shi kuma likita, duk lokacin da sai da cuta ta zama chronic ta kuma yi attack sannan za ku kai masa majinyaci, to hakan ya fi bata masa rai domin ya san ko tantama babu sai an yi asarar kudi mai ciwo.

Wanda da an kawo wannan marar lafiyar tun da wuri, da tuni wani labarin ake yi, domin za su bashi kulawar da in Allah ya amince ba lallai cutar ta ci karfinsa ba kamar yadda ta ci karfinsa yana gida.

Ya kamata mu gyara.

Previous Post Next Post