![]() |
Shugaba |
Ina yi muku maraba.
Yau, a cikin wannan dandali, za mu tattauna ne akan shugabanci sannan za mu yi bayani akan shugaba.
Shugabanci na daya daga cikin abubuwa masu girman gaske a gargajiyance da musulunce.
Wannan dalilin ya sa ba a zabar mutum shugaba har sai ya hada wadansu qualities, abinda aka rasa mafi akasari tattare da shuwagabannin wannan zamani.
Shugabanci amana ce, amma fa yanzu abin sai dai a yi kurum! Domin wasu gyade suke yi masa sannan su yi amfani da kotu wurin rufe masa baki.
Shugabanci
“Shugabanci wanda wasu ke kira da ‘Jagoranci’ na nufin shugabantar jama’a ko mulkarsu walau a gargajiyance, a siyasance, a addinance ko kuma ta wata hanyar.”
Waye Shugaba
“Shugaba wani bawan Allah ne wanda Allah ya bai wa amanar al’umma ya jagorancesu.”
Hakika zama shugaban jama’a ba karamin abu ne mai girma ba, domin kusan kowanne nauyi na wadannan mutane yana rataye a wuyan shi shugaban.
Hakan yasa, da jama’armu masu neman shugabanci ruwa-a-jallo za su yi masa kallon ta natsu, to, lallai da sun sassauta neman shugabancin da suke ko-ta-wanne-hali.
Kuma akwai wadansu nagartoci da ake bukatar samu ga kowanne shugaba, duk da cewa yanzu haka wadansu shugawabannin sai dai a yi kurum!
Nagartocin da Ake Bukata ga Shugaba
- Ilimi: Ya zama wajibi shugaba ya kasance mai ilimi, domin wannan ilimin shi zai taimaka masa wurin tafiyar da sha’anin mulkinsa bisa tafarki mai tsari ba tare da hauma-hauma ba.
- Gaskiya: Ya zama wajibi shugaba ya kasance mai gaskiya, yana kyamar satar kayan al’umma ko ta wacce siga.
- Tsare Mutuncin Kai: Dolen-dole shugaba ya tsare mutuncin kansa domin kara wa kansa mutunci kuma al’umma su ga mutuncinsa. Ba a son shugaba wanda ya cika sakin kai kawai sabon sakarai.
- Adalci: Wajibi shugaba ya zama adali, ya rinka kwatanta adalci a tsakanin wadanda yake mulka. Komai zai aiwatar, sai ya kokarta wurin iyar da shi bisa adalci.
- Yarda da Kai: Shugaba na da bukatar ya yarda da Allah kuma ya yarda da kansa domin sauran mabiyansa ma su yarda da shi. Domin in har ya yarda da kansa to zai iya tunkarar manyan kalubalalluka kuma ya ci galaba a kansu.
- Bayyan Aikace-aikacensa: Wajibi ne shugaba ya rinka bayyana aiyukan da yake gudanarwa a fili domin al’umma su san me ke wakana, kada ya barsu cikin duhu.
- Jajircewa: Dole sai shugaba ya yarda da kansa sannan zai zama jajirtacce, shi yasa matakin farko da ake bukatar shugaba ya taka shi ne; ya yarda da kansa, bayan haka sai ya zama jajirtacce wurin ganin ya iyar da aiyukan da ke gabansa.
- Iya Hulda da Jama’a: Ana da bukatar shugaba ya iya hulda da jama’a. Domin in har ya iya hulda da jama’a to hakan zai sanya kaunarsa a cikin zuciyar talakawansa ko wadanda yake jagoranta. Mu’amala wata aba ce ga shugaba!
- Mai Kirkira: Wajibi ne ga shugaba ya kasance kwakwalwarsa tana kawo wuta, duk lokacin da ya ga sabon abu sai ya kawo wa al’ummarsa muddin na cigaba ne. In kuma wadansu kirkire-kirkire ne sai ya daure gindi wurin ganin an samar da su domin amfanuwar al’umma.
- Kyautatawa da Ladabtarwa: Kowa na son mai kyauta, ina ga kuma shi wannan mai kyautar ya kasance shugaban al’umma ne? Lallai farin jininsa zai rubanya hawa-hawa. Shi yasa wajibi shugaba ya kasance mai kyautatawa al’ummarsa ta kowacce irin siga, amma fa hakan ba shi ke nufin sai ya bude kofar baitulmali a yi ta barna a ciki ba.
Har-ila-yau, dolen-dole shugaba ya kasance mai ladabtarwa. Ita kuma ladabtarwar ba dole sai kai tsaye zai aiwatar ba.
Misali: Ya tsaya tsayin-daka wurin ganin an tsayar da doka-da-oda domin rage munanan aiyuka da barna.
Ya tsaya tsayin daka wurin ganin al’umma sun bi doka, ta hanyar amfani da hanyoyi mabambanta wurin ilmantar da su mecece doka, kuma me yasa ya zama wajibi ga al’umma su bisa.
Kammalawa
Hakika shugabanci, zama shugabaa, nagartocin da ya kamata shugaba ya kasance yana da su kai har zuwa yadda zai gudanar da shugabancin nasa abu ne mai girman gaske.
Domin in son samu ne ma sai a rubuta littafi game da hakan domin yin bayani akan shugabanci na gari.