Yadda Ake Samun Kudi a Internet

Samun Kudi a Internet
Samun Kudi a Internet


Hakika akwai hanyoyi da dama wadanda ake bi wurin samun sulalla a yanar gizo (internet).

Yau, abin da za mu tattauna a kai kenan, domin zan yi muku cikakken bayani akan wadannan hanyoyi.

Sharar Fage

Matasa da dama musamman na karnin nan na 21 na da matukar son ci a huce, kuma ba laifinsu ba ne, zamani ne ya zo da hakan.

Duk wanda kaji ya fada maka cewa, "ai ba a  samun kudi a intanit."

Kada ka yarda ka musa masa, domin ko ka musa masa ba lallai ya yarda da "eh gaskiya ne ana samun alkhairi a yanar gizo ba".

Har sai ka nuna masa sakamako ra'ayil aini, ya gani kuru-kuru kudi ya shigo kuma ta yanar gizon ne.

To, ta haka za ka tabbatarwa da wawan da yace ba a samun kudi a yanar gizo abinda ka fada masa gaskiya ne.

Ko da wasa, kada ka yi zaton ba a samun kudi a yanar gizo, amma dai ka yi sani cewa, shi fa samun kudi a yanar gizo ba sauki gareshi ba.

Kafin Haka

Zan so share maka wani tunani kafin mu je kan gundarin abinda ya sada mu a shafin nan nawa.

"Samun kudi ta yanar gizo ya fi na zahiri sauki."

Babu wani sauki da ke tattare da samun kudi ta yanar gizo.

Asali ma, mental stress, da lack of activity stress su kadai sun ishi mutum kayan nauyi yayin da ya mayar da hankalinsa ga neman kudi ta yanar gizo.

Mental Stress

Shi ne cajin kwakwalwa. 

Sabgar online na dauke da cajin kai, eh man.

Dole za ka kwala idanunka kana kallon screen, kana rubutu, ko kana editing ko dai kana wani aikin daban, hakan kuma akwai gajiyarwa.

Lack of Physical Activity

Madadin neman kudi na zahiri, dole sai kana motsi, ka shiga ta can, fita ta can, za ka rinka motsa jikinka yayin da kake fafutukar neman taro da sisi.

Amma shi neman kudi online, yana son ka samu wuri guda ne ka zauna na lokaci mai tsawo kana aiki.

Hakan kuma kan sanya jiki ya saki, bisa wannan dalili ya zama wajibi ga wanda ya shirya sabgar neman kudi ta yanar gizo to ya rinka fita gudun motsa jiki, kwallo da sauransu domin zazzagar da kitsen da ka iya zama a jikinsa samakamkon rashin katabaus.

Commitment

Dole akwai bukatar sadaukar da lokaci, da kuma mai da hankali wurin yin wannan abun da ka sa a gabanka.

Sabgar samun kudi ta yanar gizo na da bukatar commitment.

Kada ka rinka yi wa sabgar shan ruwan tsuntsaye muddin da gaske so kake ka mayar da harkar da ka sa a gabanka sabgar neman abinci. 

Hanyoyi 5 Na Samun Kudi a Internet

Akwai hanyoyi sama da 100 wadanda ake bi wurin samun kudi a yanar gizo.

Na zabo wadannan guda 5 din ne domin kusan su ne masu sauki kuma wadanda kusan kowa zai iya muddin ya sa kansa.

1. Youtubing

Shi ne kirkira da kuma dora bidiyo a YouTube. Babbar hanya ce ta samun kudi ta yanar gizo.

Da fari za ka bude channel, ka saita ta, ka cike dukkanin bayanan da ake bukata.

Sai ka sayi kayan daukar bidiyo, ka fara dauka.

Ka nemi mai editing ya maka edit na bidiyoyinka, ko ma ka yi da kanka.

Daga nan sai ka dora a tasharka ta YouTube. 

Bayan ka dora, tsugunne ba ta kare ba. Sai ka yi kwafi na link din ka fara sharing a social media kana turawa abokai da 'yan'uwa domin su kalla.

Kafin ka tara mabiya, ana daukar lokaci, kuma ana shan wahala.

Amma da zarar ka yi nasarar kafa tashar YouTube ta ginu, kai ne da jin dadi ba wani ba.

Kuma shi ma ana yi masa SEO, don haka sai ka yi maza ka koyi SEO na YouTube domin bidiyoyinka su rinka samun masu kalo a kyauta.

2. Blogging

Yana daya daga cikin fitattun dadaddun hanyoyin samun kudi ta yanar gizo. Blogging sana’a ce ta yin rubuce-rubuce a shafin yanar gizo akan abubuwa mabambanta.

Amma in son samu ne, mutum ya dauki shiyya daya kamar beauty da fashion, autos, technology, news, how to, food ko dai wani sashe wanda ya san yana da sha’awa a kansa sai ya fara rubutu a kai.

Kafin ka fara harkar blogging, kana da bukatar ka fara iya bincike, domin rubutu ba ya yiwuwa gaba-gadi har sai marubucin yana yawan karance-karance.

Kuma ka san SEO, yadda za ka tsara article dinka, ka san yadda za ka bude shafin yanar gizo ka dora masa domain ka saita shi.

Sannan ka dora shi a Search Engines domin ka rinka samun free organic traffic. 

In kuma ba ka iya ba, sai ka samu wanda ya iya kirkirar shafukan yanar gizo ya hada maka wanda kake so da irin features din da kake bukata.

A Najeriyarmu, mutane da dama sun yi arziki da harkar blogging, irin su Makinde Azee mai shafin NaijaLoaded, Linda Ikeji mai shafin LinkaIkejisBlog da sauransu.

Sai dai, harkar blogging aba ce wacce ke da bukatar hakuri da kai zuciya nesa, domin za ka iya share shekaru biyu cirr ba tare da ka samu taro ba.

Amma fa daga ranar da abubuwa suka bude, shi kenan kai kuma ka zama kudi.

3. Crypto

Da yawa daga cikin matasa sun san harkar kirifto, in ba su santa a zahirance ba, sun santa a baki.

Harka ce ta saye da siyar da kudaden lantarki kamar su bitcoin, ethereum, ripple, litecoin, usdt da sauransu.

Saboda tsanin kasadar da wannan kasuwa ta kirifto ke dauke da ita, shi yasa ba a shigarta gaba-gadi sai da malamin da zai fahimtar da mutum kasuwar.

In ma baka da malami, sai ka iya tsantsar tsagwaron bincike a kan kasuwar da turanci, ta haka za ka hadu da kwararru a harkar wadanda za su taimaka maka ko da kuwa ba ka san su ba.

Kamar yadda harkar crypto ke dauke da takadiriyar kasada, haka take da riba, amma fa sai in mutum bai fada cikin drip ba.

In dai muradinka samun kudi ta yanar gizo ba tare da ka sha wahala kamar masu blogging da youtubing ba, to ka fara kirifto.

4. Forex Trading

Kasuwar forex babbar kasuwa ce ta samun kudi, amma ita mafi akasarin lokuta cinikin kudaden kashashen waje ake yi a cikinta sai kuma saye da siyar da hannun jari na kamfanunuwa.

Mutane da dama na saye-da-sayar da kudaden kasashen duniya suna kuma samun alheri sosai.

Kasuwar dai kamar kasuwar canji ce ta wafa amma ta yanar gizo.

Haka kuma ta kasuwar forex za ka iya yin amfani da broker wurin sayen hannun jari, in ya kara daraja ka siyar.

Sai dai zan so ka yi sani cewa, ba a shiga kasuwar forex ba tare da ilimin kasuwar ba.

Yana da kyau ka fara karatu da bincike a kan kasuwar kafin ka mata dirar mikiya, kuma kada ka zuba kudin da ba za ka juri asararsu ba.

5. e-Commerce

Shi dai e-Commerce kasuwanci ne amma na digital, wato saye da siyarwa ta yanar gizo.

In dai so kake ka samu kudi ta yanar gizo, to me zai hana ka fara sayar da kayayyaki ta shafukan sada zumunta, da shafukan yanar gizo?

Kai hatta awara ma yanzu ana iya yin odarta sannan a kawo maka ita a take-away.

Saboda haka za ka iya juyar da kasuwarka da kake yi ta zahiri ka hada da yanar gizo, duk wadanda suke zagi-zaginku, ko birninku za su iya oda sai ka aike musu da kaya bayan sun turo kudi.

Da son samu ne, ku fara da yin bincike akan e-commerce domin ku kara samun ilimi a kai, sannan sai ku fara ta inda kuke so.

Kammalawa

Ba fa iya su kenan ba, wadannan na zakulo su ne domin sun fi kowadanne saukin farawa.

Za ku iya fadada bincikenku da kuma yin abun a aikace.

Previous Post Next Post